<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>507</hymn_number>
<title>Ranar Ubangiji LW507</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ranar Ubangiji fa tana zuwa babu shakka.
 Al'umma duniya za su rushe
 Masu aikata mugunta ranar su tana zuwa
 Kamin ranar nan ka cece ni.

[V2]
 KORUS
 I, gani nan Yesu na zo.
 Ina neman ceto
 Ka ji tausayi ka cece ni
 Yesu gani ka cece ni.

[V3]
 2) Za mu ji ƙarar ƙafo daga can samaniya
 Mai cetonmu yana sabkowa
 Tare da mala'iku za su ware masu bi
 Kamin ranar nan ka ceci ni.

[V4]
 Korus
 (Karatu : I Tas 4 : 15-16)

[V5]
 3) Masu bi da sun mutu daga ikon duniya
 Za su fara jin ƙarar ƙafo
 Waɗanda suke da rai daga nan za su tashi
 Kamin ranar nan ka ceci ni.
 Korus

[V6]
 4) Rana za ta yi dufu, taurare na faɗuwa
 Samaniya tana sabkowa
 Wata za ya ki bada haske babu sauren salama
 Kamin ranar nan ka ceci ni.
 Korus</lyrics>
</song>